XtGem Forum catalog
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Imam Ali (a.s) Da Mu'awiyya

SASANTAWA (DON TSAYAR DA SHUGABA)

Bisa la'akari da fitinar da ta kunno kai cikin rundunar Imam Ali (a.s) sanadiyar daga Alkur'ani mai girma guda 500 da sojojin Mu'awiyya suka yi don yaudara da kuma neman tsagaita wuta, hakan ya tilasta Imam Ali (a.s) yarda da a tattaunawa don sasantawa tsakanin bangarorin biyu.

Don haka sai mutanen Sham (mabiya Mu'awiyya) suka zabi Amr bn al-As a matsayin wanda zai wakilce su, saboda irin wayo da iya makircin da aka san shi da shi. Su kuma mutanen Iraki (mabiya Imam Ali) sai suka zabi Abu Musa al-Ash'ari sakamakon matsin lambar wasu wawaye wadanda suke da wasu maslahohi cikin rundunar Imam Ali (a.s), don kuwa Abu Musa mutum ne mai karancin wayo, ban da ma cewa shi ne ya tsige Ali daga matsayinsa(1).

Wasu ruwayoyi suna nuni da cewa rikicin da ya kunno kai cikin rundunar Imam Ali (a.s) ya kai matsayin da har wasu suna masa barazanar za su aikata abin da suka yi wa halifa Usman bn Affan a kansa, ko kuma su mika shi ga Mu'awiyya(2).

Don haka sai aka shirya za a tattauna da fitar da matsaya tsakanin wakilan biyu (Amr bn al-As da Abu Musa al-Ash'ari). Lokacin da suka hadu don tattaunawa, sai Amr bn al-As ya yi wayo wa Abu Musa ya gabatar masa da shawarar tsige Imam Ali (a.s) da Mu'awiyya tare daga matsayin da suke kai. Saboda haka lokacin da Amr bn al-As ya ga Abu Musa ya amince da wannan shawara tasa sai ya bukace shi da ya fara tsige wanda yake wakilta (Imam Ali) yana mai cewa bai kamata ya gabaci sahabin Manzon Allah (s.a.w.a) ba.

Ta haka ne Amr bn al-As ya yi wayo da ha'intar Abu Musa al-Ash'ari, ya bar shi cikin mamaki, duk kuwa da cewa Abdullahi bn Abbas ya ja kunnensa da ya yi hankali da ha'incin bn al-As.

Don haka sai Amr bn al-As ya nada Mu'awiyya, hakan kuwa ya faru ne a shekara ta 37 hijiriyya.

Shi kuwa Amirul Muminina Ali (a.s), lokacin da ya ga wayon da Ibn al-As ya yi wa Abu Musa da kawo karshen wannan tattaunawa ta hanyar da ba ta dace ba saboda ha'incin Ibn al-As - kamar yadda muka gani - sai Imam (a.s) ya bukaci da a sake komawa fagen fama yana mai cewa:

"Ya ku jama'a! Hakika na umarce ku da wani al'amari dangane da wannan taron sasantawa, kuka saba min. Na rantse, lalle sabo na gadar da nadama. Matsayata da taku kamar yadda mawakin Hawazin yake cewa ne:

Na baku umarnina a Mun'arijillliwa,Amma ba ku ga kyaun shiryarwata ba sai da gari ya waye.

Wadannan masu sasantawa guda biyu sun kauce wa Littafin Allah, sun kashe abin da Alkur'ani ya raya sannan kuma suka raya abin da ya kashe. Dukkansu biyun sun bi son zukatansu ba tare da shiriya ta Ubangiji ba. Sun yi hukumci ba tare da wata hujja ba, ba kuma tare da dogaro da wani hadisi ba, don haka dukkansu suka bace. Sai suka barranta daga Allah, ManzonSa da kuma salihan bayi. Don haka ku shirya wa jihadi, ku shirya kanku don bin tafarkin gaskiya, ku wayi gari a matsayarku(3)".

MURDA-MURDAR MU'AWIYYA

Bayan yakin Siffin da al'amarin hukuncin nan, Mu'awiya ya fara gudanar da al'amurra kamar shi ne cikakken mahukunci, sai ya fara tara dukiya, zakka da haraji, yana aikawa sojoji suna yankuna don firgita mutane da shimfida mulkinsa a yankuna dabam daban. Har ila yau Mu'awiya zabarwa rundunarsa wasu mutane masu laifuka, wadanda ba su da wata gabatuwa a Musulunci, ya nada su kwamandoji; kai wadanda ma ke dauke da kiyayya ga Musulunci, ya kuma ba su kayayyakin ta'addanci wadanda suka saba ko ta ina da abubuwan da Manzo (s.a.w.a) ya kasance yana wasici ga sojojinsa da su.

A shekara ta 40 bayan hijira, Mu'awiya ya hada wata runduna mai mayaka dubu uku, karkashin jagorancin Busir bin Arda'a, ya hore shi da ya bi hanyar Hijaz, Madina, Makka har ya kare da Yaman, inda ya ce masa:

"Kar ka sauka a garin da mabiyansa ke biyayya ga Ali har sai ka shimfida musu harshenka da barazana, har sai sun ga cewa ba matsera gare su daga gare ka, kuma (su ga) cewa kai kana kewaye da su, sannan sai ka kira su da su mika bai'a gare ni, duk wanda ya ki ka kashe shi; ka kashe 'yan shi'ar Ali duk inda suke (4)". Ya taba yiwa mutane sallar asuba raka'a hudu a lokacin yana cikin maye.

Hakika kuwa Busir ya aiwatar da horon shugabansa Mu'awiya da duk nau'o'insa (horon), har ma ya kara barna da laifuka don kara samun shiga a wajen shi (Mu'awiyan); yayin da ya shiga neman duk wanda ke da wilaya ga Ali ko Sahabbansa, da duk wanda ya jinkirta yin mubaya'a (ga Mu'awiya), ya rika kona gidajensu yana rusa su, yana kwace dukiyoyinsu. Adadin wadanda ya kashe a zuwa da dawowa sun kai mutum dubu talatin ya kuma kona wasu mutane da wuta, kan haka ne ma mai wake ke cewa:

Duk inda Busra ya tafi da rundunarsa
Busra ya karkashe da kona iya iyawarsa(5).

Har ma lokacin da ya je Hadhramaut, cewa ya yi: "Ina so in kashe rubu'in (wato kashi daya bisa hudun) mutanen Hadramaut".

Haka nan Mu'awiya ya hori Sufyan bin Auf al-Gamidi da ya shiga Iraki, yana mai masa wasici da ya kwace dukiyoyi ya kuma yi kashe-kashe da kone-kone, inda ya ce masa:

"Ka rushe duk kauyen da ka wuce, ka kashe duk wanda ka hadu da shi daga wadanda ba sa bisa ra'ayinka, ka kwace dukiyoyi, domin haka ya yi kama da kisa, ya ma fi zafi ga zukata".

Sufyanu kuwa ya aiwatar da wasiyyoyin Mu'awiya har da kari a kai; yayin da ya yi wa ma'abuta amana (daga Ahlulkitabi) diran-mikiya, ya kashe su, ya kwace dukiyoyinsu; su ne kuwa wadanda Manzon Allah ya yi wasici da a kiyaye su, da cewa shi da kan shi (s.a.w.a) zai ja da duk wanda ya cutar da su.

Wannan karamin misali ne daga yadda Mu'awiya da mabiyansa suka gudanar da al'amurransu. Mu'awiya ya takaita manufofinsa da dalilin yake-yakensa a cikin hudubarsa ga mutanen Kufa, bayan sulhu da Imam Hasan (a.s), inda ya ce:

"Wallahi ban yake ku don ku yi azumi, ko don ku yi hajji ko don ku bayar da zakka ba, domin ai kuna aikata duk wadannan; ni na yake ku ne don in mulke ku da karfin tsiya".

Wannan shi ne tarihin Mu'awiya. Sabanin haka, Imam Ali (a.s) ya kasance yana wasici ga ko wane kwamandansa da yake aikawa don dakatar da hare-haren Mu'awiya da cewa:

"Ka ji tsoron Allah wanda kake tafiya zuwa gare Shi, kar ka wulakanta Musulmi ko kafirin alkawari, kar ka kwace dukiya ko da ko zuriyya ko da za ka tafi a kafa kuwa, kuma ka kiyaye yin salla a kan lokacinta".

Dubi yadda yake wasici ga ko wannensu da kiyaye mutuncin mutane, Musulmi da wadanda ba Musulmi ba. Don haka rikicin Imam Ali (a.s) da Mu'awiya rikice ne na hanyoyi biyu kishiyoyin juna: tafarkin gaskiya da kyawawan halaye mai kalubalantar tafarkin bata da batarwa da zalunci da kisan-mummuke. Ba kuwa yadda za a yi wadannan hanyoyi biyu su taba haduwa.

____________

(1)- Sibt Ibn Jawzi cikin Tazkirat al-Khawas, shafi na 96 da A'ayan al-Shi'a na Muhsin Amin, juzu'i 3, shafi na 199.

(2)- Tazkira al-Khawas shafi na 95.

(3)- Tazkira al-Khawas shafi na 103.

(4)- Al-Thakafi, al-Gazat, shafi na 598.

(5)- Al-Gazat, shafi na 598.

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din